Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Condo

Mutane dubu dari 2 sun karbi rigakafin Ebola a Congo

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, ta ce jami’an lafiya sun bai wa mutane sama da dubu 200, maganin rigakafin kamuwa da cutar Ebola daga farkon watan Agusta da muke ciki zuwa yau.

Fiye da mutane dubu 2 cutar ta Ebola ta hallaka a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo bayan sake barkewarta karo na 10 a bara
Fiye da mutane dubu 2 cutar ta Ebola ta hallaka a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo bayan sake barkewarta karo na 10 a bara Reuters/Baz Ratner
Talla

Bayanai daga kwamitin da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kafa don yaki da cutar ta Ebola na nuni da cewa, wannan kokari ya biyo bayan lakume rayukan mutune kusan 2000 daga kusan 3000 da ake zargin sun kamu da cutar ne.

Masana sun yi bayanin cewa wannan annoba Ebola da ta sake bulla a kasar a watan Agusta, ita ce ta biyu mafi muni a tarihin cutar Ebola, tun bayan da ta bayyana daga shekarar 2014 zuwa 2016 a Afirka ta Yamma, inda ta yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 11.

Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jinkai ta Amurka a makon da ya gabata ta ce za ta samar da kudaden wadata allurar rigakafin cutar Ebola da ake kira V920 ga kamfanin Merck and Co Incorporated, kuma har ila yau akwai allurar rigakafi da kamfanin Johnson and Johnson ta samar amma hukumomi ba su kai ga rabarwa ba, saboda gudun rikita al’ummar ke a razane.

Da alama an shawo kan cutar Ebola a birnin Goma, amma ban da sauran sassan Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, inda ma’aikatan lafiya ke fama da rashin tsaro da yada labaran karya a dandalin sadarwa na intanet dabam – dabam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.