rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barazanar 'yan aware a Kamaru ta tilastawa jama'a tserewa

media
Shugaban 'yan awaren Kamaru Julius Sisiku Ayuk Tabe YouTube

Rahotanni daga kasar Kamaru na nuni da cewa dubban al'ummar da ke yankin masu amfani da turancin Ingilishi na ci gaba da tserewa sakamakon barazanar ‘yan aware na ci gaba da kaddamar da hare-hare.


Wasu majiyoyi dai na bayyana cewa Mayakan 'yan awaren masu fafutukar sun sha alwashin kaddamar da hare-hare a muhimman wurare da ke kasar ta Kamaru bayan hukuncin daurin rai da rai kan shugabanninsu.

A makon jiya ne dai wata kotun soja ta zartaswa shugabannin masu fafutukan awaren su 10 hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, matakin da masana ke ganin kaiya harzuka mayakan kungiyar 'yan awaren.

Wani mazaunin yankin Muntari Hamisu ya tabbatarwa da sashen hausa na Radio France International rfi faruwan lamarin ya na mai cewa hatta kudin motar safara daga yankin zuwa sauran sassan kasar sai da ya yi tashin gwauron zabi.

A cewar Muntari Hamisu ficewar jama'a daga yankin 'yan awaren na da nasaba da yadda suka dakatar da harkokin karatu bayan kulle ialhirin makarantun yankin, matakin da ya sanya iyayen da ke son 'ya'yansu su samu karatu tserewa.

Rahotanni sun bayyana cewa al'ummar yankin da dama sun razana da barazanar ta 'yan aware.