Isa ga babban shafi
Japan-Afrika

Shugabannin Afrika 20 sun hallara a taron bunkasa nahiyar a Japan

Fiye da shugabannin nahiyar Afrika 20 ne yanzu haka suka hallara a birnin Yokohama na kasar Japan dai dai lokacin da taron bunkasa nahiyar ya kankama karkashin jagoranci shugaba Shinzo Abe.

Taron bunkasa nahiyar Afrika a birnin Yokohama na Japan
Taron bunkasa nahiyar Afrika a birnin Yokohama na Japan RFI Hausa
Talla

Taron wanda aka fara shi a yau Laraba 28 ga watan Agusta za a karkare shi ne ranar juma’a 30 ga watan nan, wanda kuma zai bayar da damar cikakkiyar tattaunawar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika da kasar Japan.

Taron wanda aka kirkireshi tun a shekarar 1993 kuma ya ke gudana duk bayan shekaru 5 na tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tattalin arziki dama ci gaba kasashen nahiyar ta Afrika.

Kawo yanzu shugabannin da suka hallara a Yokohama sun hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou sai Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya kana Azali Assoumani na tsibirin Comoros da kuma Danny Faure da tsibirin Seychelles.

Sauran sun hada da Alpha Conde na Guinea da Patrice Talon Jamhuriyyar Benin da kuma Julius Maada Bio na Sierra Leone kana Andry Rajoelina na Madagascar da kuma Ismail Omar Guelleh na Djibouti sai Joao Lourenco na Angola.

Cikin jerin shugabannin akwai kuma Hage Geingob na Namibia da George Weah na Liberia da Felix Tshisekedi na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da Uhuru Kenyatta na Kenya baya ga Yoweri Museveni na Uganda da kuma Abdul Fatten Al-Sisi na Masar kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afrika da kuma Paul Kagame na Rwanda da Mohamed Abdullahi Farmajo na Somalia da Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe.

Akwai kuma Faure Gnassingbe na Togo da Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na Ghana da Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu da Ibrahim Boubakar Keita na Mali baya ga Edgar Lungu na Zambia da kuma Macky Sall na Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.