rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Tattalin Arziki Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Afrika na kashe dala biliyan 50 kan sayen abinci - AFDB

media
Wata katafariyar gona a tarayyar Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Bankin raya kasashen Afrika AFDB, ya fitar da wata kididdiga da tace cikin shekara guda, kasashen nahiyar na kashe kusan dala biliyan 50 wajen sayo kayayyakin abinci daga turai da sauran kasashen ketare.


Mataimakiyar shugabar kula da sashin bunkasa noma, na bankin Jennifer Blanke ce ta bayyana haka, yayin taron hadin gwiwa na tattalin arziki da aka kamala jiya Juma’a a birnin Tokyo na kasar Japan.

Yayin kokawa kan halin da kasashen na Afrika ke ciki kan batun wadatar abinci, Blanke ta ce abin takaici ne su rika kashe makudan kudaden wajen shigo da abinci daga waje duk da albarkar kasar noman da suke da ita.

Wani binciken masana ya nuna cewa kasashen Afrika ke da kaso 60 daga cikin 100 na fadin kasar noma a duniya.