Guterres ya roki yan tawayen ADF
Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterresh, da ya soma ziyarar kwanaki uku a Jamhuriyar Congo ya roki mayakan kungiyar yan tawayen ADF da su yiwa Allah sun ajiye makamai.
Wallafawa ranar:
Guterres ya soma ziyarar a ne garin Goma, babban birnin lardin arewacin Kivu.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya roke su da su bayar da hadin kai don tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki da kasar baki daya.
A karshe Antonio Gutteres ya yi kira ga jami’an kiwon lafiya tareda yaba musu dangane da jajircewar su wajen yaki da cutar Ebola.
A dai-dai lokacin da Guterres ke ziyarar kasar ,Ministan tsaron kasar ya fitar da wasu alkaluma dake bayyana adadin sojan kasar da suka rasa rayukan su a yaki da kungiyar ADF,akala sojoji 1662 suka mutu a yakin da kasar ke yi da yan ADF kama daga shekara ta 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu