rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Cote d'Ivoire Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masoya Dj Arafat sun fasa akwatin dake dauke da gawar

media
Jana’izar Dj Arafat a Abidjan na kasar Cote D'Ivoire REUTERS/Thierry Gouegnon

Gwamnatin Cote D’Ivoire ta karrama marigayi kuma Shahararren mawakin zamanin Cote d’Ivoire DJ Arafat wanda ya rasu sakamakon hatsari babur .


An dai gudanar da addu’o’i tareda girmama marigayin Dj Arafat  a filin wasa na Felix Houphouet Boigny na Abidjan ,duban jama’a daga gida da waje ne suka halarci wanan gangami.

Dj Arafat wanda ya yi suna sakamakon salon rawa da waka da ake yiwa taken coupé-décalé, yana da dimbim magoya baya a kashen duniya .

Yan lokuta da isar da akwatin dake dauke da gawar a makabarta, magoya bayan sa suka fitar da akwatin inda suka fasa akwatin don tabbatar da cewa Dj Arafat ne cikin sa.

An ji masoyan nasa suna ta kuka, tareda fadin cewa, “ba zai yiwu Arafat ya mutu ba”.

An haifi Ange Didier Huon da aka sani da Dj Arafat a shekarar 1986.