Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya

A Alhamis dinnan Afirka ta Kudu ta sanar da rufe ofisoshin jakadancinta da ke biranen Abuja da Lagos a Najeriya, biyo bayan hare – hare da tarzoma na ramuwar gayya kan kadarorin ‘yan kasar da suka auku a Najeriya sakamakon hare – haren kin jini da ’yan kasashen waje ke fuskanta a Johannesburg.

Shugaban Nanjeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa bayan hare-haren kin jinin baki kan 'yan Najeriya a birnin Johannesburge
Shugaban Nanjeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa bayan hare-haren kin jinin baki kan 'yan Najeriya a birnin Johannesburge Pulse
Talla

Kakakin ma’aikatar horkokin wajen Afrika ta Kudu, Lunga Ngqengelele ya ce, ‘’bayan mun samu rahotanni da barazana daga wasu ‘yan Najeriya, mun yanke shawarar rufe ofisoshin jakadancinmu a kasar yayin da muke ci gaba da nazari kan yadda al’amura ke tafiya.’’

Ya ce shawarar dakatar da ayyuka na zuwa ne bayan wasu gungun matasa sun yi kokarin balle ofishin jakadanci kasar da ke Lagos a Najeriya.

Kasashen biyu sun tsaurara matakan tsaro tun bayan aukuwar lamarin.

An shiga zaman tankiya ta fuskar diflomasiya tsakanin kasashen biyu dake da kima a nahiyar Afrika, bayan Najeriya ta ayyana bijire wa taron tattalin arziki na duniya kan Afrika a birnin Cape Town na Afrika ta Kudu, wadda da ma mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo zai halarta.

A ranar Talata Najeriya ta gayyaci jakadan Afrika ta Kudu a kasar kan wannan batu, sannan a Laraba ta bayyana janye jakadanta a Afrika ta Kudu, byan ta bayyana matukar rashin jin dadinta game da halin da’yan kasarta ke ciki ga shugaba Cyril Ramaphosa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.