rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon shugaban ECOWAS zai mayar da hankali kan samar da tsaro

media
Sabon shugaban ECOWAS Mahamadou Issouffou SIMON MAINA / AFP

Sabon Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS Mahamadou Issofou ya bayyana batutuwan da zai mayar da hankali a kai da suka hada da tsaro da zaman lafiya da kuma inganta dimokiradiya da hadin kan kasashen dake yankin.


Shugaba Issofou, wanda har ila yau shine shugaban Jamhuriyar Nijar, da aka nada ya jagoranci kungiyar ranar 29 ga watan Yuni, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci cibiyar kungiyar da ke Abuja, inda yake cewa kungiyar zata taimaka wa kasashen dake cikin ta wajen shirya karbabben zabe.

Issofou ya bayyana manyan matsalolin da suka addabi yankin da suka hada da ayyukan ta’addanci da fashi a kan teku da kuma kungiyoyin da ke aikata manyan laifuffuka, yayin da ya bayyana shirin gudanar da taron kungiyar na musamman ranar 14 ga watan Satumba a Burkina Faso, wanda zai mayar da hankali kan matsalar tsaron da ake fama da shi a Yankin Sahel.

Shugaban kungiyar ya bayyana muhimmancin inganta harkokin noma da samar da abinci, lura da cewar akasarin mazauna yankunan karkara a kasashen sun fi mayar da hankali.