rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Samuel Eto'o yayi ritaya daga fagen kwallon kafa

media
Samuel Eto'o tsohon dan wasan Kamaru Courtesy of Konyaspor

Fittacen dan wasan kwallon kafar Kamaru da ya lashe kyautar dan wasa mafi fice a Afirka har sau 4 Samuel Eto’o yau ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 38.


A sakon da ya aike ta kafar Instagram, Eto’o yace lokaci yayi da zai bude wani sabon babi a rayuwar sa, inda ya gode daukacin magoya bayan sa da wadanda suka taimaka masa wajen samun nasara a rayuwar sa ta kwallo.

Eto’o ya lashe kofin zakarun Turai sau 2 tare da Barcelona, yayin da ya lashe kofin La Liga sau 3 kafin ya koma kungiyar Inter Milan.

A Milan ya lashe kofin zakarun Turai da gasar Serie A da kuma Coppa Italia a shekara guda, kafin ya koma kungiyar Anzhi Makhachkala dake Rasha.

Daga bisani Samuel Eto’o ya yiwa kungiyoyi irin su Chelsea da Konyaspor da Qatar Sports wasanni.

Tsohon dan wasan ya kuma lashe kofin Afirka sau biyu da Kamaru.