rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mahajjatan Najeriya sun tsallake rijiya da baya

media
Wasu Mahajjatan Najeriya Solacebase

Akalla mahajjatan jihar Benue a Tarayyar Najeriya 550 ne suka tsallake rijiya da baya sakamakon hadarin da jirginsu ya kusa fuskanta jiya asabar matakin da ya tilasta masa saukar gaggawa a filin jirgin sama na Minna da ke jihar Niger.


Rahotanni sun bayyana cewa Jirgin kirar Boeing 747-400 ya gamu da tangardar Inji ne lokacin da ya ke da tafiya bayan kwaso mahajjatan daga kasa mai tsarki, ko da dai babu rahoton rasa rai ko mummunar jikkata.

Wasu ganau sun shaida cewa mahajjatan sun rika fita da gaggawa daga jirgin saboda fargabar iya kamawarsa da wuta bayan saukar ta gaggawa.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa sassan jikin jirgin da dama sun lalace matakin da ya tilasta aikewa da kwararru don duba lafiyarsa gabanin sake bashi damar daukar jama’a.