Isa ga babban shafi

Fafaroma ya karkare ziyararsa ta Afrika a Mauritius

A Litinin Shugaban mabiya darikar katolika paparoma francis ke ziyarar zango na karshe a tsibirin Mauritius daga cikin jerin kasashen Afrika 3, inda ake sa ran ya jinjina wa hadin kai da mutunta juna tsakanin alumma daya, duk da banbance banbancen su.

Fafaroma Francis a Mozambique
Fafaroma Francis a Mozambique REUTERS/Grant Lee Neuenburg
Talla

Dubban mabiya darikar katolika ne suka taru a port Louis, babban birnin kasar, suna dakon isar shugaban su Fafaroma Francis ya yi jawabi a tsibirin India da ta kasance inda kungiyoyin addinai da na kabilu ke haduwa don tattaunawa.

Josette da ta kasance daya daga cikin masu jiran isowar paparoma, ta ce sama da mutane dubu 3 da dari 5 ne suka fito daga tsibirin Reunion, mai nisan kilometer 175 daga Mauritius.

Ita kuwa Genevieve mai shekaru 47 yar asalin kasar Mauritius ta bayyana wannan taro a matsayin babba, yayin da ta ce haduwarsu da Fafaroma Francis na da matukar muhimmanci.

Kashi 30 cikin 100 na al’ummar Mauritius krista ne, wadanda mafi yawa daga cikin su mabiya darikar katolika ne. saidai Cardinal Maurice Piat, bishop na majami’ar Katolika a babban birnin kasar, ya ce ziyarar shugaban ba ga mabiyansa kadai ba ne, amma ga illahirin alummar kasar masu mabanbantan addini.

Kasar Mauritius dai ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1968, kuma a halin yanzu ta kasance cikin kasashe mafi arziki a nahiyar Afrika, sabanin Mozambique da Madagaskar, kasashe mafi talauci a fadin duniya da shugaban ya ziyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.