rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boko Haram ta kashe Sojojin Najeriya da dama

media
Dakarun Najeriya dake yaki da yan kungiyar Boko Haram AFP Photo/ISSOUF SANOGO

Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojoji da dama ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin kwonton bauna da mayakan Boko Haram suka kai masu kusa da garin Gudumbali da ke jihar Borno a ranar litinin da ta gabata.


Harin na zuwa ne bayan da sojojin ke kan hanyarsu ta kai dauki ne ga wasu sojojin Najeriya da na Chadi da ke kokarin kwace garin na Gudumbali daga ‘yan Boko Haram, inda mayakan suka yi amfani da mayan makamai ciki har da rokoki a kansu, shaidu sun ce an kashe sojoji gommai tare da lalata motoci da makamansu.

Wannan harin na dada nuna ta yada yan Boko Haram ke ci gaba da zama babbar barrazana ga gwamnatin Najeriya.