rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uganda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Uganda za ta fara hukuncin kisa kan wadanda suka yi kisan kai

media
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni ya bukaci aiwatar da hukunci daidai da abinda mutuum ya aikata domin rage yaduwar aikata laifuffuka, bayan kashe wani dan uwan sa.


Uganda yanzu haka na fama da manyan laifuffuka da suka hada da kisa da fashi da makami da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, yayin da al’ummar kasar ke korafin cewar 'yan Sanda basa iya hukunta wadannan laifuffuka saboda cin hanci da rashawa.

Shugaba Museveni ya bayyana aniyar sa na aiki tare da kotuna domin gaggauta hukunta wadanda ake zargi da aikata laifuffukan, wanda zai kunshi kashe wanda aka samu da aikata laifin kisa.