rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ba shida niyar jefa yan Najeriya cikin kunci

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP

Kwana guda bayan da Gwamnatin Najeriya ta sanar da kara harajin VAT daga kashi 5 zuwa sama da kashi 7 kan kayayyakin da jama’a ke saye a fadin kasar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar bashi da aniyar jefa yan kasar cikin kuncin rayuwa.


Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar shugabannin kungiyar kwadago ta TUC, inda yake cewa gwamnatin zata cigaba da lalubo hanyar saukakawa jama’ar kasar halin kuntsin da suke ciki.

Shugaban ya jaddada aniyar gwamnatin sa na aiwatar da shirin karin sabon albashi.

Yan Najeriya na sa ran wadanan sauye-sauye zasu kawo sauyi a rayuwar su ta yau da kullum.