Isa ga babban shafi
Kamaru

Yanayin lafiyar shugaban rediyo da talabijin Kamaru da ke tsare ya tabarbare

Yanayin lafiyar tsohon shugaban rediyo da talabijin mallakin gwamnatin kasar Kamaru Amadou Vamoulke da ke tsare a gidan yari yau shekaru uku na ci gaba da tabarbarewa.

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya REUTERS/Carlo Allegri -/File Photo
Talla

Vamoulke, wanda sau 21 kotu na dage sauraren shari’ar da ake yi masa bisa zargin kashe kudade ba a kan ka’ida ba, kungiyar kare ‘yan jaridu RSF ta ce akwai bukatar bayar da dama domin duba lafiyarsa.

Kungiyar mai zaman kanta ta ce tana da rahoto kan lafiyar wanda ake zargin da ke nuni da cewa yana matukar bukatar a duba lafiyarsa.

A shekarar 2005 aka nada Amadou Vamoulké a matsayin shugana gidajen rediyo datalabijin na Kamaru, kuma a watan Yulin shekarar 2016 aka kama, yana kan mukamin na sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.