Isa ga babban shafi

ECOWAS za ta kaddamar da shirin yakar ta'addanci na shekaru 4

Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun sanar da wani kudirin hada hannu wajen yaki da ta’addanci da su ke fuskanta wanda zai lakume biliyoyin daloli, yayin babban taronsu da aynzu haka ke gudana can a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso.

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS FEMI ADESINA
Talla

Taron na ECOWAS wanda a wannan karon ya samu karuwar kasashen Chadi da Mauritania ana sa ran ya kaddammar da sabon shirin yaki da ta’addancin yayin karkare taron.

Shirin wanda kawo yanzu ba a bayyana adadin kudin da zai lakume ba, ana sa ran ya fara aiki daga shekarar 2020 zuwa 2024.

Dama dai taron a wannan karon dai, an yi hasashen zai mayar da hankali ne kan barazanar tsaro da ke kara karfafa a kasashen yankin yammacin Afrikan, yayinda ake saran Muhammadu Buhari na Najeriya ya gabatar da jawabi don neman hadin gwiwar takwarorinsa kasashen yanki a yaki da ta’addanci da karancin tsaro.

Yanzu haka dai shugabannin sun kammala hallara a Wagadugu, yayinda Mahamadou Issoufou na Nijar kuma shugaban kungiyar ke jagorantar bude taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.