rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi wa gawar Robert Mugabe bankwanan karshe

media
Akwatingawar tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ana yi masa bankwana a ranar 13-09-2019 ®REUTERS/Siphiwe Sibeko

Shugabannin kasashe da dama ne suka halartar taron don girmama gawar tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da aka gudanar jiya asbar a filin wasan birnin Harare.


Daga cikin wadannan suka halarci wadannan addu’o’in sun hada na Kenya Uhuru Kenyatta, na Afirka ta Kudu Cyrl Ramaphosa, sai Denis Sassou Nguesso na Congo Brazzaville da kuma Obiang Nguema na Equatorial Guinea.

Hakazalika akwai tsoffin aminan shugaban da suka hada da Kenneth Kaunda na Zambia, Olusegun Obasanjo na Najeriya da kuma Joaquin Chissano na Mozambique da suka halarci taron.

To sai dai bayan wadannan addu’o’i, har yanzu ba a bayyana ranar da za a rufe gawar tsohon shugaba Mugabe ba, wanda ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.