rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

ECOWAS CEDEAO Sahel

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dala milyan dubu daya don yaki da ta'addanci a yammacin Afirka

media
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré (H) na zantawa da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou a taron CEDEAO A Ouagadougou, 14-09-2019. ISSOUF SANOGO / AFP

Shugabannin kasashen Yammancin Afirka sun amince da wani shirin yaki da ayyukan ta’addanci da za a kashe dalar Amurka milyan dubu daya tsakani 2020 zuwa 2024 a yankin.


Shugaban kuma shugaban kungiyar Ecowas-Cedeao Nijar Issoufou Mahamadou, shi ne ya sanar da haka a karshen taron da ya samu halartar shugabannin yankin na yammacin Afirka jiya asabar a birnin Ouagadougou na Burkina Faso, inda ya ce kasashen yankin ne za su tara wadannan kudade domin tafiyar da wannan aiki.

Har ila yau kasashen Mauritaniya, Kamaru da kuma Chadi, wadanda ba mambobi ba ne a kungiyar ta Cedeao sun halarci wannan taro tare da daukar alkawarin bayar da tasu gudunmuwa.

Shugabannin na Ecowas sun ce za a yi amfani da wadannan kudade ne domin karfafa rundunonin kasashen da kuma rundunar G5-Sahel.

A lokacin taron kungiyar ta Ecowas da za a yi cikin watan disamba mai zuwa ne za a fayyace yadda shirin zai gudana.

Kafin wannan yunkuri na kungiyar Ecowas, tuni kasashen biyar na yankin Sahel wato Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da kuma Nijar suka sanar da kafa runduna ta musamman G5-Sahel domin fada da ayyukan ta’addanci, to sai dai rashin kudi ya hana wannan runduna fara aiki kamar yadda ya kamata.