rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

‘Yan gudun Hijira Italiya Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jirgin agajin Ocean Viking ya samu izinin ceto 'yan cirani

media
Jirgin agaji na Ocean Viking Hannah Wallace Bowman/MSF/Handout via REUTERS

Jirgin agaji na Ocean Viking ya samu izinin dawo da aikinsa na ceto ‘yan cirani daga gabar ruwan Libya, bayan matakin Italiya na janye tsarin kin bayar da mafaka ga ‘yan cirani wadda ta amince da dakko ‘yancirani 82 daga tsibirin Lampedusa a jiya Asabar.


Babbar jami’ar da ke kula da aikin agajin jirgin na Ocean Vikin Nicola Stalla ta ce za su ci gaba da aikin gajin la’akari da yadda tarin jama’a ke rasa rayukansu a tekun a kan hanyarsa ta shiga nahiyar turai don samun ingantacciyar rayuwa.

Tuni da Italiya ta gudanar da gwajin lafiya kan ‘yan ciranin 82 bayan da suka shafe kwanaki 6 a tsakiyar teku.

Yanzu haka dai kasashen Italiya Faransa da Jamus sun amince da karbar ‘yan cirani 24 kowannensu yayinda Portugal za ta karbi 8 kana Luxembourg ta karbi 2.