rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tunisia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Tunisia na dakon sakamakon zaben shugaban kasa

media
'Yan takarar neman kujerar shugabancin kasa a Tunisia Arab.com

Dai dai lokacin da al'ummar kasar Tunisia ke dakon sakamakon zaben shugaban kasar da suka kada kuri'a a jiya Lahadi, biyu daga cikin 'yan takarar da da basu da alaka da gwamnati sun bayyana samun nasara, tun a sa'o'i kalilan bayan rufe rumfunan zaben irinsa na 2 a kasar tun bayan juyin juya halin 2011.


Hukumar zabe a kasar ta Tunisia ta bayyana cewa kashi 45 na masu rijistar zabe ne suka kada kuri'unsu a zaben, matakin da ke nuna yadda aka samu raguwar masu kada kuriar kasa da kashi 64 da aka samu a 2014.

Kais Saied, masanin harkar shari'a da dokokin kasa da ya shiga zaben a matsayin dan takara mai zaman kansa, ya bayyana cewa shi ke kan gaba da yawan kuri'u, kamar yadda alkaluman farko suka nuna.

Magoya bayan Nabil Karaoui da ake tsare saboda zargin halarta kudaden haramun, na ta bayyana farin ciki a Ofishin yakin neman zabensa, bayan ya bayyana samun nasarar zuwa zagaye na biyu, duk da ya ke an gudanar da zaben ya na tsare.

Sauran fitattun 'yan takara sun hada da AbdelFatah Mourou da ke yiwa Jam'iyyar Ennahda takara, sai kuma Firaminista Youssef Chahed.

A gobe Talata ne ake sa ran bayyana cikakken sakamakon zaben.