rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin ta'addanci ya hallaka Sojin Kamaru 6

media
Wasu dakarun sojin kasar Kamaru. AFP PHOTO/STRINGER

Akalla Sojin Kamaru 6 suka gamu da ajalinsu bayan wani kazamin harin bazata da mayakan Boko Haram suka kaddamar kan sansanin Sojin hadin gwiwa don yaki da ta'addanci da ke garin Sureram na yankin tafkin Chadi bangaren kasar.


Majiyoyin Labarai a Kamaru sun ruwaito kwamandan rundunar hadin gwiwar Birgediya Janar Bouba Dobekreo na cewa mayakan na Boko Haram sun isa sansanin ne a jiragen kwale-kwale da kuma babura tare da farmakar sansanin da ke tsibirin Sureram na lardin Arewa mai nisa cikin tsakaddaren Asabar wayewar jiya Lahadi.

Janar Bouba ya tabbatar da mutuwar dakarun sojin kasar 6 a harin baya ga wasu soji 8 da suka samu raunuka ko da dai Kwamandan bai bayyana ko sojin sun yi nasarar hallaka ko kuma kama mayakan na Boko Haram ba.

Sai dai Janar Bouba ya bayyana cewa an yi zazzafan gumurzu tsakanin dakarun Sojin da mayakan na Boko Haram.

Harin na jiya Lahadi na jerin hare-hare mafiya muni da kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar kan dakarun kasar ta Kamaru, bayan na watan Yuni da ya hallaka sojin kasar 17 tare da fararen hula 7 a garin Darak duk dai a yankin na Tafkin Chadi.

A baya bayan nan Boko Haram na tsananta hare-hare cikin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi tare da kashe tarin jama'a galibi Sojoji ciki har da hari kan Sojin Najeriya da Nijar da kuma Chadi baya ga na Kamaru.