rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tunisia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Tunisia ta ki ba da belin Karoui don shiga zagayen zabe na 2

media
Dan takarar neman kujerar shugaban kasa a Tunisia Nabil Karoui AFP/Fethi Belaid

Kotu a Tunisia ta ki amincewa da bayar da belin Nabil Karoui, domin shirin zuwa zaben shugaban kasa zagaye na biyu, sakamakon nasarar da ya samu a zaben da aka yi a karshen mako.


Lauyan Karoui, Kamal Ben Masoud yace zasu daukaka kara, bayan da alkalin kotun yace bashi da hurumin bada belin.

Ana tuhumar dan takarar ne da halarta kudaden haramun, kuma bisa dokokin kasar yana da hurumin tsaya takara har sai kotu ta same shi da aikata laifi.