rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Benin Togo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya na iya katse lantarkin da ta ke bai wa Nijar Togo da Benin

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Twitter/Asorock

Kasashen Nijar Togo da Jamhuriyar Benin ka iya fuskantar karancin lantarki kowanne lokaci daga yanzu matukar basu dauki matakin biyan bashin wutar lantarkin da Najeriya ke binsu ba.


Najeriya wadda ke fuskantar matsalar wutar lantarki a yankunanta tsawon lokaci yanzu haka ta kafa wani kwamiti da zai gano abinda ya hana ruwa gudu a wannan fanni.

Sai dai bayan gudanar da binciken kwamitin ya bayyana cewa babbar matsalar da ke hana ruwa gudu wajen samarwa kamfanonin kasar wadataciyar wutar da zasu dogara bai wuce nauyin da ta ke dauka wajen bai wa wasu kasashen ketare lantarkin ba.

A cewar kwamitin kamfanin samar da lantarki na kasar Nijar Nigelec da kuma na Benin Ceb sun gaza biyan tarin basukan da Najeriyar ke binsu wanda da kudaden za ta yi amfani wajen inganta bangaren lantarkin na ta.

Tun kafin yanzu dai, Najeriyar ta yi barazanar katse lantarkin da ta ke bai wa kasashen 3 duk da sanadin tarin bashin da ta ke bin kasashen da suka gaza biya tsawon lokaci.