rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Burkina Faso Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu mahara su kashe sojojin Burkina Faso

media
Sojojin Burkina Faso a arewacin kasar AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO

Wani harin da ‘yan bindiga suka kai a cikin daren jiya Alhamis waye wa safiyar yau juma’a a yankin arewa maso gabashin Burkina Faso ya halaka sojin kasar akalla biyar tareda raunata soja daya.


Rahotanni daga Burkina Faso na bayyana cewa maharani dauke da mugan makamai sun kai harin kwantar bauna zuwa ayarin sojojin Burkina Faso dake sintirin tsaro a kauyen TOENI na yankin Sourou inda nan take sojojin Burkina Faso 5 suka rasu yayin da wani dayan ya samu rauni.

Haka zalika a cikin daren na alhamis zuwa Juma’a, wani harin da aka kai da wani abu mai fashewa ya lalata gadar Boukouma wada ta raba garuruwan Djibo da Dori manyan biranen biyu na arewacin kasar ta Burkina Faso.

Wata majiyar tsaro ta sheidawa kanfanin dillanci labarai Faransa AFP cewa,jim kadan bayan harin hukumomin Burkina Faso sun tura karin sojoji a yankin da harin ya auku don kakkabe sauran ‘yan bindigar

Wanan harin na zuwa ne akalla mako guda,da kasar ta Burkina faso ta karbi taron kungiyar raya tattalin kasashen Afirka ta ECOWAS kan batun yaki da ta’addanci.

Tun farkon Shekara 2015 hare-haren ‘yan ta’adda suka tsananta a Burkina Faso dake cikin jerin kasashe mafi talauci a yammacin Afirka, inda wasu alkalumma suka bayyana adadin mutanen da suka mutu 570 biyo bayan hare-haren yan ta’adda a Burkina Faso.