Isa ga babban shafi
Afrika

WHO ta zargi Tanzania da boye wadanda ke dauke da Ebola

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta zargi hukumomin kasar Tanzania da kin gabatar da bayanai kan wadanda ake zargin suna dauke da cutar ebola, matakin da ake ganin yana iya yiwa yaki da cutar zagon kasa.

Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola
Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola REUTERS/Baz Ratner
Talla

Hukumar tace ta samu labarin dake bayyana cewar an samu mai dauke da cutar a Tanzania ranar 10 ga wannan wata, kuma har an killace shi a Dar es Salaam, yayin da wasu bayanai suka ce an sake samun Karin mutane biyu dake dauke da cutar.

Sanarwar hukumar lafiyar tace duk kokarin da suka yi na neman bayani daga gwamnatin Tanzania abin yaci tura, inda a ranar 14 ga wata Gwamnati ta rubuta wasikar cewar babu wani mai dauke da cutar.

Kasashen dake gabashin Afirka sun dauki matakan sa ido sosai saboda barkewar cutar a Congo, wadda tayi sanadiyar kasha mutane sama da 2,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.