rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yara 9 sun mutu bayan rugujewar wata makaranta a Kenya

media
Masu aikin ceto bayan rugujewar ginin wata makaranta a Kenya. Kenya Red Cross

Akalla kananan yara 7 aka tabbatar da mutuwarsu yayinda wasu da dama kuma suka jikkata bayan rugujewar wani ginin makaranta a birnin Nairobin kasar Kenya.


Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Kenya Cyrus Oguna ya ce kaw yanzu gawar yara 9 su ke da ita, sai kuma karin wasu kananan yaran 57 da suka samu raunuka.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbin faduwar ginin ko da dai wasu na alakanta shi da tsufa ko kuma rashin inganci.

Yanzu haka dai masu aikin ceto na ci gaba da lalubo yaran da suka nutse a baraguzan gine-gine wadanda kawo yanzu ba a kai gano adadinsu ba.