rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun kashe mutane a Burkina Faso

media
Yan Sanda a wasu yankunan kasar Burkina Faso ISSOUF SANOGO / AFP

Hukumomin Burkina Faso sun ce akalla mutane 9 aka kashe lokacin da yan bindiga suka kai wasu hare hare guda biyu a yankunan dake fama da tashin hankali.


Sanarwar tace an kai harin farko ne ranar asabar a Pissele dake kusa da Bourzanga, inda aka kashe mutane 6, yayin da aka kai hari na biyu a kauyen Bool-Kiiba inda aka kashe mutane 3.

Burkina Faso ta fada cikin tashe tashen hankula tun bayan kawar da shugaba Blaise Compaore daga karaga mulkin kasar, inda aka kashe mutane sama da 580 daga shekarar 2015 zuwa yanzu.