Isa ga babban shafi
DR Congo-Ebola

Za a soma alurar hana kamuwa da cutar Ebola

A karo na biyu a cikin kasa da watanni biyu Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo zata gudanar da alurar riga kafin hana kamuwa da annobar cutar Ebola a farkon watan Oktoban bana, kamar yadda hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta sanar .

Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Congo
Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Congo Reuters/Baz Ratner
Talla

Daraktan hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yabawa matakin da gwamnatin Congo ta dauka a matsayin dattako da kuma jajircewa wajen kokarin da take wajen kawo karshen annobar.

Hukumar lafiyar ta MDD ta bayyana gudanar da aikin gwajin magani na biyu, da kamfanin Johnson & Johnson na kasar Amruka ya samar, wanda ake bukatar a gudanar da shi sau biyu a cikin kwanaki 56 bayan gudanar da bada maganin farko ga mutanen da ke fuskantar barazanar yiyuwar harbuwa da cutar a yankunan kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da ba a samu bulluwar cutar ba a baya.

To sai dai kungiyar likitoci ta Médecins Sans frontières MSF ta zargi hukumar Lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya da dogara da maganin da cibiyar binciken magungunna Merck ta samar ne, magani daya tal da ake amfani da shi a halin yanzu wajen dakile yaduwar annobar ta Ebola da ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 2.100.

A watan yulin da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana daga alkaluman barazanar cutar ta Ebola da cewa ta tsallake kasar ta Congo zuwa matsayin mai barazana ga duniya.

Annobar ta Ebola da ta sake bayyana a watan ogustan 2018 da ta gabata, ita ce ta biyu mafi girma a tarihi, baya ga wace ta hallaka mutane 11 a kasashen Guinnee, Sierra Leone da Libéria a tsaknin 2014 zuwa 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.