rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Osinbajo zai je kotu don kare kansa

media
Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo. Solacebase

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yace a shirye yake ya jingine kariyar da dokar kasa ta bashi daga tuhuma domin zuwa kotu danganin an hukunta mutanen dake masa Kazafi domin ganin sun bata masa suna.


Yayin da ya ke mayar da martani kan zargin da wani tsohon jami’in Jam’iyyar APC, Timi Frank ke masa, na cewar hukumar tara kudaden haraji ta kasa ta bashi makudan kudaden da yayi amfani da su wajen yakin neman zaben da akayi a farkon wannan shekara, Osinbajo ya bayyana zargin a matsayin abin takaici.

Mataimakin shugaban kasar ya ce ya ba da umurnin daukar matakan shari’a a kan Timi Frank da Katch Ononuju da sunayen su ya bayyana kan kazafin bata masa sunan.

Osinbajo yace zai tube rigar kariyar da kundin tsarin mulki ya bashi domin zuwa kotu don ganin ya wanke kan sa.

Ita ma hukumar tara kudaden haraji ta Najeriya tayi watsi da zargin wanda ta bayyana shi a matsayin rashin hankali.