rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki Tarayyar Afrika Duniyarmu A Yau

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afrika na tafka hasarar sama da dala biliyan 200 duk shekara - Buhari

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya, a taron kasashe karo na 74 a birnin New York. 4 ga Satumba, 2019. REUTERS/Carlo Allegri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kasar ta tafka hasarar kimanin dala biliyan 157, wadanda ya ce zurarewa suka yi a dalilin laifukan almundahanar da aka tafka, tsakanin shekarun 2003 da 2012.


Buhari ya ce sace biliyoyin dalolin ya taka muhimmiyar rawa wajen jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin kangin talauci.

Shugaban ya kuma kara da bayyana kaucewa biyan haraji, a matsayin daya daga cikin matsalolin almundahanar kudaden da kasashen Afrika ke fuskanta, inda yace wani rahoton hukumar sa ido kan biyan haraji da kuma asusun bada lamuni na duniya IMF, ya ce kasashe masu tasowa na tafka hasarar sama da dala biliyan 200 duk shekara, sakamakon yadda manyan kamfanoni suke kin biyan haraji ga gwamnatocin kasashen da suke gudanar da ayyukansu.

Buhari ya bayyana alkalumman hasarar da Najeriya gami da nahiyar Afrika ke tafkawa ne yayin wani taron hadin gwiwa, na hukumar bunkasa ci gaban kasashen Afrika dake karkashin kungiyar kasashen nahiyar AU, da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC.

Taken taron hadin gwiwar na Afrika shi ne ‘Karfafa alakar kasashen duniya wajen yakar almundahanar kudade da kuma kwato kudade da kadarorin da aka sace’.

Taron ya gudana ne a gefe guda, yayinda shugabanni da kuma wakilan kasashe, ke taro a zauren majalisar dinkin duniya a birnin New York.