rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Robert Mugabe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An binne Mugabe a Kutama

media
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe marigayi Robert Mugabe. REUTERS/Philimon Bulawayo

An kammala birne gawar tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yau Asabar a kauyensa na haihuwa Kutama bayan shafe tsawon makwanni ana takaddama kan inda za a birne shi tsakanin Iyalansa da Gwamnatin kasar.


Bikin birne gawar Mugabe wanda ya mutu tun a farkon watan nan ya na da shekaru 95 a duniya, ya gudana ne ba tare da halartar tururuwar jama’a ba.

A ranar Juma’a Iyalan Mugabe suka yi nasarar samun izinin birne shi a kauyen da aka haife shi wato Kutama mai nisan kilomita 90 daga Harare babban birnin kasar ta Zimbabwe.

Marigayi Robert Gabriel Mugabe wanda aka Haifa a yankin Kutama, na kudancin Rhodesia (kasar Zimbabwe a yanzu) ranar 21 ga watan Fabarairun 1924 ya yi kaurin suna ne sanadiyyar kakkarfar kiyayyar da ya nuna ga turawan mulkin mallaka bayan gwagwarmayarsa ta neman ‘yanci.