rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Somalia Tarayyar Turai Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kai hare-hare kan sojin Amurka da EU a Somalia

media
Kungiyar al-Shebab ta dauki alhakin kaddamar da farmaki kan sojojin Amurka da ayarin sojin Kungiyar Tarayyar Turai REUTERS/Feisal Omar

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamar da farmaki kan sansanin sojin Amurka da kuma ayarin motocin dakarun Kungiyar Tarayyar Turai a Somalia.


Mayakan Al-Shebaab sun yi amfani da bama-bamai wajen far wa sansanin sojin Amurka da ke garin Baledogle mai tazarar kilomita 110 daga yankin arewa maso yammacin birnin Mogadishu, yayin da kuma suka bude wa sojojin wuta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Litinin, Al-Shebaab ta ce, wasu kwararrun mayakanta ne suka kaddamar da harin, yayin da ta kara da cewa, har yanzu ana kan dauki-ba-dadi.

Garin Baledogle na dauke da babban sansanin da sojin Amurka ke amfani da shi wajen kai wa Al-Shebaab harin jirgi mara matuki.

A bangare guda, an yi amfani da mota makare da bama-bamai wajen kai hari na biyu kan dakarun Kungiyar Tarayyar Turai da ke bayar da horo ga sojojin Somalia a birnin Mogadishu.

Wani jami’in tsaron Somalia, Omar Abikar ya ce, motar makare da bama-baman ta tarwatse bayan ta yi karo da ayarin motocin dakarun na Turai

Wakilin Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ce, ya ga motar yaki mai silke dauke da tutar Italiya da aka lalata a sanadiyar harin.

Ma’aikatar Tsaron Italiya ta tabbatar da kai wa ayarin na dakarun Turai harin, sai dai babu cikakken bayani kan sojin da suka samu rauni ko mutuwa.