rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ko muhawara ta kasa za ta kawo karshen rikicin Kamaru?

media
Shugaban Kamaru Paul Biya na fatan muhawarar za ta kawo karshen rikicin 'yan awaren kasar. REUTERS/Mike Segar

Kasar Kamaru ta bude zaman muhawara ta kasa a wannan Litinin da zummar kawo karshen rikicin ‘yan aware da ke yankin masu magana da Turancin Ingilishi duk da cewa, jagororin ‘yan tawayen kasar sun ki shiga wannan muhawara.


Za a ci gaba da gudanar da muhawarar karkashin jagorancin Firaminista, Joseph Dion Ngute har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba a wani babban dakin taro da ke birnin Yaounde.

Shugaba Paul Biya da ya shafe shekaru 37 kan karagar mulki, na fatan wannan muhawara za ta kawo karshen rikicin da ya haifar da tarnaki ga tattalin arziki kasar mai noman Kofi da Koko.

Sai dai gabanin fara wannan muhawara, da dama daga cikin masu rajin kare hakkin bil’adama da masharhanta sun bayyana shakkunsu, inda suke ganin taron ba zai yi tasiri ba.

Kusan mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu, yayin da rabin miliyan suka kaurace wa gidajensu tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2017 tsakanin jami’an sojoji da ‘yan tawayen kasar da ke rajin ballewa daga Kamaru domin cin gashin kansu.