rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An saki jagoran 'yan adawan Kamaru Maurice Kamto

media
Maurice Kamto, jagoran 'yan adawan Kamaru MARCO LONGARI / AFP

An saki jagoran ‘yan adawan Kamaru Maurice Kamtodaga gidan yari a Asabar din nan, bayan wata kotun soji ta yi umurnin a sake shi, biyo bayan take – taken hakan da shugaban kasar Paul Biya ya yi.


Wata kotun soji a Kamaru ta bada umurnin sakin jagoran ‘yan adawan kasar Maurice Kamto, wanda ya shafe tsawon watanni 9 yana tsare bayan jerin matakan sasantawa da shugabn kasar Paul Biya ya dauka.

Kotun ta ce ana iya sakin Kamto da wasu mutane 101 su yi tafiyansu, idan har an tsare su babu gaira ba dalili ne.

Lauyan Kamto Sylvain Souop ya ce ‘’mun yi na’am da sakin abokan huldar mu wadanda tun da farko bai kamata a tsare su ba’’.

A ranar Juma’a Biya, wanda ya shekara 37 yana jagorancin Kamaru ya ce ya yi umurnin da a sauke zarge – zargen da ake wa shugabannin ‘yan adawa.

Kamto ya gurfana gaban kotun soji da shi da wasu mutun 88 a watan Satumba bisa zargin yhin fito – na – fito da gwamnati, tada hankalin kasa ta hanyar tawaye, zarge – zargin da hukuncinsu ka iya zama kisa.