Isa ga babban shafi

Sai Najeriya ta inganta masana'antu ne tattalin arziki zai gyaru- Dangote

A Najeriya fitattun masana tattalin arziki ‘yan kasuwa da manyan ma’aikatan banki sun fara wani yunkurin hada hannu wajen bai wa gwamnati gamsassun shawarwari kan yadda za a magance kalubalen da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote.
Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Yayin babban taron tattalin arzikin Najeriyar karo na 25 da ke gudana a Abuja babban birnin kasar, Aliko Dangote fitaccen attajirin nahiyar Afrika, ya ce bangaren masana’antu Najeriya na tallafawa ne da kashi 9 kacal cikin dari maimakon akalla kashi 30 da ya kamata ace bangaren na samarwa tattalin arzikin kasar.

A cewar Aliko Dangote fitaccen dan kasuwa kuma masanin tattalin arziki, matukar za a bunkasa bangaren masana’antu a kuma gyara hanyoyin sufuri musamman bangaren jiragen kasa baya ga fadada tashoshin ruwan kasar don saukaka hanyar fita da kuma shigo da halastattun kayaki babu shakka zai taimaka matuka.

Sai dai Dangote ya ce duk da haka dole ne a magance matsalar fasakwauro wadda ke yiwa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa tare kuma da bunkasa bangaren iskar gas da kuma samar da gyara a bangaren musayar kudade.

A nasa bangaren Mai martaba sarkin Kano fitaccen masanin tattalin arziki kuma tsohon shugaban babban bankin Najeriya Muhammadu Sanusu na II yayin jawabinsa gaban taron ya ce har yanzu yawan al’ummar Najeriya bai kai matsayin da za a iya alfahari da shi wajen samar da ci gaba ba, yana mai cewa tattalin arziki ba zai taba daidaituwa ba, har sai al’umma ta daidaitu.

Sarkin na Kano ya gwada misali da yadda yawan ‘yan Najeriya ya zama babbar barazana ga tsaron kasar baya ga tattalin arziki wanda a cewarsa ke neman zama yawan tsintsiya ba shara.

A cewar tsohon Gwamnan babban bankin Najeriyar maukunta na gaza kula da al’umma ta yadda su ke juye barazana ga tsaro,musamman a yanzu yadda al’amura masu alaka da garkuwa da mutane baya ga hare-haren ‘yan bindiga ke kara ta’azzara.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada shugabar First Bank Mrs Ibukun Awosika, da shugaban Majalisar tattalin arziki EAC Dr. Doyin Salami baya ga Atedo Peterside.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.