Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kaddamar da tawagar mashawartansa kan tattalin arziki

A Karon farko a cikin shekaru 4, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da Majalisar bashi shawara kan Tattalin Arziki da zata dinga baiwa gwamnati shawarwarin da suka shafi yadda za’a inganta tattalin arzikin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da manbobin tawagar kwararru masu bashi shawara kan tattalin arziki.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da manbobin tawagar kwararru masu bashi shawara kan tattalin arziki. Femi Adeshina/ Presidency
Talla

Yayin kaddamar da Majalisar, Buhari ya shaidawa wakilan ta cewar babu wani mutum guda da yake da ilimi ko sanin komai da zai iya magance matsalolin da suka addabi Najeriya, saboda haka aka zabo su domin bada gudummawar irin kwarewar da suke da ita domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, a dai dai lokacin da kasar ta magance matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar lokacin da ta zo karagar mulki.

Shugaban yace ya zuwa yanzu Najeriya ta dogara ne da alkaluma da kuma binciken da hukumomin kasashen duniya suka yi wajen tsara manufofin ta, alhali kuwa kasar na da kwararrun da suka yi fice kana zasu iya bada gudummawa domin samun biyan bukata.

Ya kara da cewa akasarin shirye shiryen da suka gabatar a shekaru 4 da suka gabata, an tsara su ne domin dawo da Najeriya tafarkin cigaba, lura da halin da kasar ta samu kan ta.

Buhari ya baiwa kwamitin damar gayyatar duk wani jami’in gwamnati domin samun bayanan da suke bukata, yayin da ya kuma shaidawa Yan kwamitin cewar an basu damar daukar duk wani mutum da suke ganin zai iya bada gudumawa wajen gudanar da ayyukan su.

Shugaban Majalisar Farfesa Doyin Salami ya jaddada aniyar su ta aiki tukuru wajen ganin sun bada tasu gudummawa da zata kaiga cigaban Najeriya baki daya.

Salami yace bukatar su itace ta ganin tattalin arzikin Najeriya ya samu habaka da kuma yaduwa zuwa kowanne bangare ta yadda Yan kasar zasu ji a jikin su.

Sauran Yan Majalisun sun hada da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Farfesa Chukwuma Soludo da Dr Mohammed Sagagi da Farfesa Ode Ojowu da Dr Shehu Yahya da Dr Iyabo Masha da Mr Bismark Rewane sai kuma Dr Mohammed Adaya Salihu a matsayin Sakatare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.