Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Mahara sun halaka masallata 16 a Burkina Faso

Akalla mutane 16 suka halaka wasu 2 suka jikkata a wani farmaki da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan wani Masallaci a arewacin kasar Burkina Faso.

Mutane 16 suka halaka a wani farmaki da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan wani Masallaci a arewacin kasar Burkina Faso.
Mutane 16 suka halaka a wani farmaki da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan wani Masallaci a arewacin kasar Burkina Faso. File/AFP
Talla

Hukumomin tsaro a kasar sun ce, maharan sun afkawa masu ibadar ne a babban masallacin garin Salmossi misalin karfe 7 zuwa 8 na daren jiya Juma’a, inda suka bude musu wuta.

Duk da cewa Burkina Faso na daga cikin kasashen Afrika masu fama da hare-haren ta’addanci, mafi akasarin ‘yan kasar na adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare a kasar, musamman na Faransa da ta yi musu mulkin mallaka.

A ranar asabar da ta gabata, kimanin mutane dubu 1 suka yi zanga-zanga a Ouagadougou, babban birnin kasar, don yin Allah-wadai da ta’addanci da kuma kafa sansanonin sojojin kasashen Turai da Amurka a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.