rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Macky Sall ya gana da Abdoulaye Wade

media
Abdoulaye Wade da Macky Sall a fadar shugaban kasar dake Dakar Seyllou / AFP

A Senegal Shugaban kasar Macky Sall ya share kusan sa’o’I biyu ya na ganawa da tsohon Shugaban kasar Abdoulaye Wade a fadar Shugaban kasar dake birnin Dakar.

Shugabanin biyu sun share kusan shekaru biyar ba tareda sun gana a kai ba.


Ganawar dake a matsayin kawo karshen zaman doya da man ja da mutanen biyu keyi tun bayan saukar Abdoulaye Wade da ya shugabanci kasar Senegal kama daga shekara ta 2000 zuwa 2012.

Abdoulaye Wade da yanzu haka dan sa Karim Wade ke fuskantar tuhuma daga kotun Senegal bisa zargin sa da karkata dukiyar kasa, ya shawarci Macky Sall da ya samar da wani tsari da zai baiwa gwamnatin kasar damar sa ido zuwa batutuwan da suka jibanci Mai da iskan Gas da wasu albarkatun karkashin kasa ga baki daya.