rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun sake kai farmaki a Burkina Faso

media
Wasu jami'an sojin kasar Burkina Faso. AFP/Getty Images

Hukumomin tsaron Burkina Faso sun ce fararen hula 4 sun rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai yankin arewacin kasar.


An dai kai farmakin jiya asabar ne a garin Samboulga dake lardin Lorum, kwana guda bayan halaka mutane 16 da mayaka masu ikirarin jihadi suka yi yayinda suka ibada a babban masallacin garin Salmossi.

Har yanzu dai babu Karin bayani kan maharan, daga hukumomin tsaron Burkina Fason, zalika babu wata kungiya da ta dauki alhakin hare-haren.

A shekarar 2015, Burkina Faso ta soma fuskantar tsanantar hare-haren mayaka masu da’awar Jihadi, musamman a yankunan arewaci da kuma gabashin kasar.