rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnati da kungiyoyin kwadago sun cimma jituwa kan sabon albashi

media
Wasu mambobin kungiyar kwadago a Najeriya The Guardian Nigeria

Bayan daukar tsawon kwanaki 3 ana kai ruwa rana a wani taron tattaunawa tsakanin shugabancin kungiyoyin kwadago da gwamnatin Najeriya dangane da aiwatar da tsarin biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a kasar, bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya.


Takaddar bayan taron tattaunawar na kwanaki 3 ta kunshi bayanan da ke cewa, gwamnatin Najeriyar bisa sanya hannu ministan kwadago da samar da aikin yi, ta amince da biyan ma’aikatu da sassan gwamnati na Tarayya Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi karkashin dokar mafi karancin albashi ta 2019.

Cikin wadanda suka jagoranci cimma matsaya game da batun bayan barazanar kungiyoyin kwadago na tsunduma yajin aiki, sun kunshi ministan kwadagon Najeriyar Dr Chris Ngige tare da karamin ministan kwadago Dr Festus Keyamo.

Sauran wadanda suka sanya idanu a tattaunawar ta tsawon kwanaki 3 da ta kai ga kulla yarjejeniyar fara aiwatar da biyan sabon albashin ma’aikatan akwai Dr Folashade Yemi-Esan shugaban ma’aikata kana daraktan ma’aikatan gwamnatin kasar Mr Olusegun Olufehinti sai kuma sakatare da shugaban JNPSNC Mr Simon Anchaver da, Mr Alade Bashir.