Guillaume Soro, zai tsaya takarar shugabamcin kasar Cote d'Ivoir a 2020
Guillaume Soro, tsohon shugaban ‘yan tawayen kasar cote d’ivoire, haka kuma tsohon shugaban majalisar dokokin kasar, da ya rikide yaama dan adawa, ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugabancin kasar a 2020.
Wallafawa ranar:
Tuni dai ake ganin zai iya samun goyon bayan kungiyar Générations et peuples solidaires (GPS). Guillaume Soro ya bayyana aniyar tasa ta son tsayawa takarar ne, a cikin wata firar hadin guiwa da ta hadashi da kafafen yada labaran Faransa, a jiya, cewa da Radio France Inernatioale RFI da tashar talabijinta France 24
Kimanin shekaru 2 da suka gabata ne dai, aka samu Baraka tsakanin Guillaume Soro da shugaba Alhasan Watara, da ake ganin yana kokarin sake yin wani wa’adi na 3,a jere, duk da cewa bai furta ba haka ba, amma kuma bai kawar da yiyuwar fsake tsayawarba bayan da kundin tsarin mulkin kasar ya bashi damar yin haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu