Isa ga babban shafi

Kotu ta dakatar da daukar aikin NNPC

A Najeriya babbar kotun kasar da ke Abuja ta dakatar da Kamfanin mai na NNPC daga daukar ma’aikatan da ya ke yi a yanzu haka, bayan karar da wani lauya mai kare hakkin dan adam ya shigar da ke kalubalantar sharuddan da kamfanin ya gindayawa masu aikewa da takardun neman gurbi daga sassan kasar.

Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya
Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya RFI
Talla

Wani Lauyan Najeriyar mai rajin kare hakkin dan Adam Pelumi Ola ya bayyanawa kotun cewa, kamfanin na NNPC ya ginda tsauraran sharudda ga masu neman gurbin ciki har da haramtawa duk wani wanda shekarunsa suka kai 28 sukunin iya aikewa da takardun neman gurbi matakin da lauyan ke cewa ya sabawa sashe na 3 na dokar daukar ma’aikata ta 2009 a kundin tsarin mulkin kasar .

A Najeriyar kasar da matasa kan gaza kammala karatu akan lokaci sakamakon tsada da kuma rashawar da ta dabaibaye tsarin, galibi ‘ya’yan marasa galihu kan rasa gurabe a manyan ayyuka duk kuwa da kwarewarsu, ciki har da kamfanin na NNPC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.