Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Zaki ya tsere daga gidan adana namun daji a Kano

Rahotanni daga Jihar Kano a yankin Arewacin Najeriya, sun bayyana cewa wani zaki ya tsere daga gidan adana namun dajin jihar da yammacin jiya Asabar, matakin da ya haddasa tsoro a zukatan al’ummar da ke tsakiyar birni.

Al'ummar Kano sun shiga tsoro bayan rahoton tserewar zakin daga gidan adana namun daji.
Al'ummar Kano sun shiga tsoro bayan rahoton tserewar zakin daga gidan adana namun daji. RFI/Hausa
Talla

Da yake tabbatar da tserewar zakin Shugaban gidan adana namun dajin, Alhaji Saidu Gwadabe y ace tuni suka baza kwararru a fannin kama zakuna don lalubo inda ya buya tare da mayar da shi ma’adaninsa.

Acewar Saidu Gwadabe ko kadan batun baya da tayar da hankali, don kuwa suna da yakinin zakin ba nisa ya yi ba, yana nan a harabar gidan adana namun dajin, inda ya nemi al’umma su kwantar da hankulansu.

Saidu Gwadabe ya ce tun a jiyan masu laluben zakin suke aikin nemansa tun daga karfe 80 na dare yayinda a yau Lahadi laluben zai fara tun daga karfe 6 na asubahi.

Shugaban na gidan adana namun daji a Kano, ya bayyana cewa da zarar anga zakin akwai nau'in bindigar da za su harba masa wanda zai sanya shi barci har a yi nasarar kama shi.

Ko a shekarun baya dai gidan adana namun dajin na jihar Kano ya fuskanci tserewar Kadaji wanda shima ya haddasa tsoro a zukatan jama'a, musamman wadanda ke anguwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.