rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tunisia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kais Saied ya sha rantsuwar kama aikin shugabancin Tunisia

media
Sabon shugaban kasar Tunisia Kais Saied 路透社

Sabon shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya sha rantsuwar kama aiki yau Laraba bayan gagarumar nasararsa mai cike da mamaki a zaben kasar da ya gwabza tsakaninsa da fitattun ‘yan siyasar kasar da suka jima suna gwagwarmaya.


Kais Saied malamin makaranta wanda bashi da wata gogewa a fannin siyasa, nasarar sa a zaben Tunisia ta zo a bazata bayan da ya lashe kashi 72 da digo 71 a zaben na watan nan wanda ya zo bayan mutuwar shugaban kasar Beji Essebsi a watan Yuli.

Sabon shugaban na Tunisa wanda farfesa ne guda a fannin shari’a yayin bikin rantsar da shi a yau Laraba ya sake nanata kudirinsa na mayar da hankali kacokan kan al’amuran da suka shafi ilimi, Tsaro tabbatar da adalci baya ga gyatta alakar Tunisia da sauran kasashen duniya da kuma yakar cin hanci da rashawa.

Babban aikin da ke gaban Kais Saeid wanda ke samun goyon bayan kusan ilahirin matasan kasar, bai wuce magance matsalar tsaron da kasar ke fuskanta ba, matsalar da Kais ya bayyana da rashin ilimin da ke addabar al’ummar kasar.

Da ya ke karbar rantsuwar kama aikin, shugaba Sa’id ya nanata kalamansa na barranta kasar da zamowa ‘yar koran kasashen duniya, yayinda da ya bayyana duk wani yunkurin kulla alaka da Isra’ila a matsayin cin amanar kasa, kalaman da ake ganin su suka kara masa farin jini da yakai ga nasararsa a zaben kasar ta Tunisa.