rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shekaru 8 bayan harin Boko Haram MDD ta bude Ofishinta a Abuja

media
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya bayan harin ta'addancin shekaru 8 da suka gabata. REUTERS/NTA via

Majalisar Dinkin Duniya ta sake bude Ofishinta da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya bayan kulle shi fiye da shekaru 8 sanadiyyar wani harin kunar bakin wake a Ofishin wanda ya kai ga daukar matakin kulle shi.


Harin wanda kungiyar Boko Haram ta kaddamar a Ofishin na Majalisar Dinkin Duniya ya hallaka mutane 23 nan take baya ga jikkata wasu da dama.

A tsawon shekaru 8 da suka gabata, Majalisar Dinkin Duniyar na amfani da wasu kananun gine-ginenta ne don ci gaba da harkokinta.

Cikin sanarwar da Ofishin Majalisar ya fitar ya nuna cewa yanzu haka jamiā€™an Ofishin sun koma ayyukansu gadan-gadan a tsohon Ofishin na su mai hawa 4 a tsakiyar birnin.