Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun kolin Najeriya ta kawo karshen shari'ar Buhari da Atiku

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar ya shigar a gabanta, inda yake kalubalantar nasarar da Muhammadu Buhari na APC ya samu a zaben shugabancin kasar na watan afrilun 2019.

Muhammadu Buhari naAPC da aboklin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar
Muhammadu Buhari naAPC da aboklin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar RFIHAUSA
Talla

Shugaban Kotun, mai shari’a Tanko Muhammad, ya ce bayan share tsawon makonni biyu suna bincikar takardun da ke kunshe da korafe-korafen da jam’iyyar PDP ta gabatar a game da yadda zaben ya gudana, daga bisani sun gano cewa ba wata hujjar da jam’iyyar ta gabatar.

Saboda haka ne a cewar shugaban kotun aka yi watsi da wannan kara, bayan da illahirin alkalai bakwai suka amince da matakin.

Wannan hukunci na kotun koli ya kawo karshen shari’ar da ta hada Atiku Abubakar dan takarar PDP da Muhammadu Buhari na APC, bayan share tsawon watanni 8 a gaban kotuna daban daban na kasar.

A lokacin da aka gudanar da zaben cikin watan fabarairun da ya gabata, Muhammadu Buhari na APC ya samu 56% na kuri’un da aka kada, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu 41%.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.