Isa ga babban shafi
Afrika

Mahara sun kashe sojin Mali 53 a Indelimane

Wasu mahara dauke da makamai sun kashe sojin Mali 53 da wani dan farar hula a wani farmaki da suka kai kan wani barikin soji  dake yankin Indelimane a arewa maso gabashin kasar a jiya  juma'a, 1 ga watan Nuwamba.Harin na zuwa ne wata daya bayan wani irin sa da ya hadasa mutuwar sojoji 40.

Wasu daga cikin sojojin Maali a garin Kidal
Wasu daga cikin sojojin Maali a garin Kidal AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Harin na jiya juma'a ya raunata da dama daga cikin sojojin kasar ta Mali, maharan sun kuma samu nasarar lalata makamai da dama a wanan bariki na sojoji dake garin na Indelimane,yayinda aka bayyana cewa  gwamnati ta aike da karin sojoji da ake sa ran zasu kai dauki zuwa yankin.

Wata majiya ta tsegunta cewa maharan sun yi awon gaba da sojojin kasar ta Mali, a shekara ta 2012 kama daga watan Maris zuwa Afrilu ne kungiyar Al- Qaida ta kama wasu yankunan arewacin kasar biyo bayan  tserewa da sojojin kasar suka yi daga arewacin .

A farkon shekara ta 2013 a karkashin hadin gwiwa tsakanin Faransa da kasashen yankin Sahel ,aka samar da rundunar hadin gwiwa da zata yaki kungiyar mayakan jihadi,duk da wannan kokari kungiyoyin yan ta'ada na ci gaba da sa kai cikin kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.