rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarakunan Afrika sun baiwa Paul Biya lambar yabo

media
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya RFI/Capture d'écran

Wata kungiyar sarakunan gargajiyar nahiyar Afrika da ta gudanar da wani taro a Jamhuriyar Benin,

taron da ya samu halartar Shuwagabanin gargajiya da daga kasashen Afrika ya bukaci yan siyasar nahiyar su saka shuwagabanin gargajiya a cikin harakokin tafiyar da al’amuran mulki a nahiyar.


Har ila yau taron ya karama Shugaban kasar Kamaru Paul Biya kan kokarin da yake wajen sake samar da zaman lafiya a kasar ta Kamaru.

Shugaban wannan kungiya da ake kira Panafrican Council of Traditional and Customary Authorities PACTCA, Dada Awiyan Octave Sarkin Dahe a jamhuriyar Benin ya bayyana Shugaban Kamaru Paul Biya a matsayin mutumen dake da hangen nesa.

Shugaban kungiyar ya na mai fatan Shugabanin Afrika za su yi koyi tareda saka Sarakunan gargajiya a lamuran yau da na kullum a hukumance.