Shekaru 6 da kashe Ghislain Dupont da Claude Verlon a Mali
Ranar 2 ga watan nuwambar shekara ta 2013 ne ‘yan bindiga suka hallaka Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon, dukanninsu ma’aikatan RFI, bayan sace su a wani wuri da ke kusa da birnin Kidal na arewacin kasar Mali.
Wallafawa ranar:
Shekaru 6 bayan faruwar wannan lamari, har yanzu masu bincike ba su gano dalilan yin garkuwa da wadannan mutane balantana kisan da aka yi masu ba, kuma har zuwa yau, ba daya daga cikin mutanen da suka aikata wannan danyen aiki da aka kama ko hukuntar da shi.
A wancan lokaci dai kungiyar al-Qaida a yankin Magreb, ta fito fili inda ta dauki alhakin kashe mutanen biyu.
Duk da cewa binciken da ake gudanarwa dangane wannan lamari na fuskantar tafiyar hawainiya, to amma majiyoyi a kusa da masu binciken sun ce ana samu ci gaba daidai gwargwado.
Lambobin wayoyin da masu bincike suka samu a cikin motar da maharan suka kaurace wa bayan sun kashe Dupond da Verlon, sun bayar da damar samun karin haske a game da wasu mutane 12 da suka yi musayar wayoyi da maharan.
Ma’ikatar shari’a Faransa, na ci gaba da fadada bincike, inda tuni alkali ya bukaci kamfanonin waya na Orange Mali da Malitel a kasar Mali su ba da hadin-kai a wannan bincike, to sai dai ba a samu irin goyon bayan da ake bukata daga kamfanin Malitel ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu