rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani gini ya rufta a Lagos

media
Masu aikin ceto bayan rugujewar ginin ANDREA LEONI / AFP

A marecen jiya asabar wani gini ya rufta aunguwar Ikoyi dake jihar Lagos. Shugaban hukumar kula da agajin gaggawa a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da cewa an ceto mutane 4 daga karkashin wanan gini da ya rufta a marecen jiya.


Ginin da ya rufta, daya ne daga cikin benaye guda hudu da ake kan ginawa a Clover Court, kuma ya rufta ne a hawa na biyu daidai lokacin da ake zuba kankare. Wasu majiyoyi sun ce daya daga cikin lebarorin da ke aiki a wurin ya rasu, yayin da sauran suka samu raunuka.

Rugujewar gine-gine masu tsayi dai ba sabon abu ba ne a Najeriya don ko a watan Satumban 2014 ma akalla mutane 116 ne suka mtu bayan fadowar wani gini mai hawa 6 a jihar Lagos ciki har da 'yan kasar Afrika ta kudu 84, wanda daga bisani kuma aka gano cewa an yi ginin ne ba bisa ka'ida ba.